No media source currently available
Wata fashewa a wani masallaci dake kauyen gadan, na karamar hukumar gezawa ta jihar kano ya raunata kimanin mutane 27. Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 5 da mintuna 20 na safiya yayin sallar asubahi.
Shirin Taskar VOA na wannan makon ya duba al’amuran cin hanci da rashawa ne a kasashen Afirka. A farkon wannan shekarar, Transparency International, cikin rahotonta na 2023, ta ce yaki da cin hanci da rashawa ya fuskanci koma-baya sosai, inda a wasu kasashen, babu abunda da aka cimma a game da haka.
"Mun kama wani Mai Unguwa da ya karbi toshiyar baki har Naira dubu dari bakwai aka zo aka kashe mutane 34 a kauyensa" in ji Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda yayin wani tattaunawa na musanman da Muryar Amurka ta yi da Gwamnonin Arewacin Najeriya a birnin Washington DC.
Wannan makon, shirin LafiyarMu zai yi nazari ne akan tarin Fuka, wata cuta daga jerin munanan cututtuka masu saurin yaduwa. Sannan, wani gwajin cutar tarin Fuka yana nuna alamun kawo sauyi a maganin cutar. Mu na kuma dauke da bayanin wani kwararre a game da cutar.
Hakuri tsakanin matasa ya kan zamo abu mai matukar wuya, ta yaya matasa zasu rungumi akidar hakuri da juna, da abin da rayuwa ta zo da shi?