Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin ‘Yan Bindiga Ya Sabbaba Kisan Mutane 10 Da Garkuwa Da Masu Unguwanni 2 A Kaduna


Yan bindiga
Yan bindiga

 ‘Yan bindiga sun hallaka akalla ‘yan sintiri 8 da wasu mutane 2 a kauyukan Kakangi da Unguwan Matinja dake karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun hallaka akalla ‘yan sintiri 8 da wasu mutane 2 a kauyukan Kakangi da Unguwan Matinja dake karamar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da masu unguwannin Kakangi da Kisiya a gundumar ta Kakangi.

Wani mazaunin yankin mai suna, idris khalid, wanda ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin yace, wasu mutane ne dauke da muggan makamai suka mamaye kauyukan a jiya Alhamis suna harbin kan mai uwa da wabi.

Idris Khalid ya cigaba da cewar, ‘yan sintirin sun yi bata kashe tsakaninsu da ‘yan bindigar, inda suka hallaka da dama daga cikinsu saidai basu iya ceto masu unguwannin da sauran jama’ar ba.

A cewarsa, “a bisa al’ada, duk sa’ilin da aka yi garkuwa da mutane, ‘yan sintiri kan bi sawun ‘yan ta’addar da nufin ceto wadanda aka sacen”.

Ya kuma kara da cewar, “a wannan karon an yi rashin sa’a a aikin ceton, inda aka rasa rayukan 8 daga cikin zaratan jami’an sintirin da suka jima suna sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da tsaron al’umma”.

A cewar Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, an cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG